Monday, January 30, 2017
WACE CE ITA 36 40
WACE CE ITA 36 40
WACE CE ITA..??
WACE CE ITA..?? 36
Na Hauwa M. Jabo
**************
Na Hauwa M. Jabo
**************
Iffaah ta isa qauyensu cike da tunanin rabuwa da da iyayen farhaaan..
Goggo tayi mamakin yanda ihhatu ta chanza tayi kyau duk wani Abu da ake buqata a gurin mace ihhatunta tana dashi saidai tunda iffaat taje bata zuwa ko ina daga gida sai gida, ta natsu matuqar natsuwa, ga yawan shiru shiru da takeyi.
Ranar goggo ke tambayarta bata sami miji a birniba, goggo ni har yanxu ba Wanda yakesona,! Ta dafe qirji kardai birnin ma kin musu halinsu kin kashe kasuwarki, zancen goggo ya bata dariya, goggo Allah ne bai kawoba, hakane kuma Dan yanxu naga kin tsama yan mata, wallahi sai mai mota zaki aura kikaini makka ko? Ta amsa da sosai kuwa ta fada tana miqewa tashige daki, zan iya CE muku tunda iffaah ta dawo qauye kullum sai tayi kuka, wani Abu takeji ya tsaya mata a zuci ya tokareta ya hanata sakat, bata iya aikin komai Idan wannan abin ya motsa mata.. abinka da yarinta Sam bata gane cewa soyayyah bace, bata gane kanta Sam. sau tari takanje bayan gari ta sami bishiya ta zauna taci kukanta har ta godewa Allah, sannan ta dawo gida ba abinda yafi damunta illa rashin gane takamammen abinda yake damunta.
Wayartace tayi qara, ta dauka farahnax ce.
Hello
Ta amsa tanajin dadi
Farahnax chikin dariya take maganar bayan sun qare qaisawa, kee iffaat Yaya ya dawo dazu sai tambayar ki yakeyi, qirjintane yayi balaen bugawa sai ta tsinci kanta da zubar da hawaye, na rashin dalili ta yi shiru.
Hello hello iffo kinajina? Tanata magana amma iffaah ta kasa bata amsa, qarshe ta tsinke wayar, iffaat ta shige dan dakinta ta zauna ta rasa mi yake damunta yan watannanin Miyasa duk lokacinda take tunanin yaya farhan take shiga wani hali??
Miyasa duk taji sunanshi sai taji faduwar gaba??
Miyasa taji tanason ta Ganinshi yanxu ??
Miyasa duk ta zauna labarin sa take sonyi??
Kai tambayoyinta sunyi yawa, batada amsar ko daya. Tayi wani tsaki
Ba abinda yake daga mata hankali irin son ganin farhaan da takesonyi, Wanda ji take kamar tayi fiffike taje ta Ganshi,
Amma ba halin yin haka,
Su iffaat an fada tarkon soyayyah amma batada labari har yanxu ba tasan miye soba..
WACE CE ITA..?? 37
Na Hauwa M.Jabo
***********
Kwanaki sunja gaba har anyi sallah qarama, iffaat zata koma gidan aikinta a birni, tun lokacin da farhaaah yazo batayi waya dashiba jifa jifa tana kiran su umma ta gaidasu, kuma farahnax tana turo mata recharging wayanta.
Ta shirya tsab sai birni,
Su umma sunyi murnar zuwanta matuqa ko banza umma nasonta Dan akwai bada labarin ban dariya kamar me shi yasa daga umma har Abba zaune sukeyi tana basu labari suna kwasar dariya.
Wannan karo an samu chanxi iffaat ta dawo amma ba komai tsakaninta dasu, musamman umman farhaan kunyar su takeji! Da kuwa zaune take tasasu gaba tana basu labari suna dariya, gashi kullum tanada sabon labarin da zata bayar, bata maimaici amma yanxu Dogon motsi bata iyayi gabansu, Ashe akwai abinda zai iya chanza wannan hatsabibiyar yarinya,?? Hmmm sai soyayyah.. soyayyar da ita kanta batasan tanayiba,
Kai amma ni jabo na jinjinama duk soyayyar da tayi tasirin chanxa wannan yarinya koda ta qara wayewa yanxu...
*******
Iffaat miyasa tunda kika dawo kika daina bamu labari?? ta sunne kai qasa tayi murmushi ba komai hajiya! Nidai wannan zuwa hutu baiyimin ba yarinya duk ta susuce sai rama takeyi? Ko wani Abu ya faru bakyason fada mana??
Laaa hajiya bakomai Abba yace ki kyaleta kinsan fa ta qara girma hankali yana shigarta, duk aka saka dariya,
Farahnax ce ta shigo tare da wata yarinya kyakyawa zatakai 24yrs kyakyawace sosai, tana shigowa tace kinganta, yarinyar mai amsa sunan suhailah ta gaida su umma da abba a kunyace, ta kalleni cikin faraa tace Ashe ma qaramace sosai gata kyakyawa kuwa saidai tafini kyau da kike cewa munyi kama., umma tace ai kuwa nima sai yanxu naga wannan kama da kuke cewa sunyi, saidai yata iffaat tafi kyau, sukayi dariya gaba daya iffaat ta gaisheda suhailah umma tace kuje daki mana, suka wuce umma tace na bisu mama na tashi na bisu, anan farahnax take baiwa Suhaila labarina sunata dariya, sai nadan saki jiki dasu dama wani lokaci zaman kadaicine ke haifar mata da damuwa bata saniba..
Suna tsaka da hira wayar Suhaila tayi qara, ta dauka tana kashe murya, duk da cewa da English suke maganar hakan bai hanani fahimtar dawa take maganaba kuma mi suke fadaba, farahnax tana bani labari amma hankalina Sam baya tare da ita qirjintane ke dukan uku uku wani baqin ciki Mara dalili takeji Wanda ya haifar mata da rashin natsuwa lokaci daya, Daidai nan kunnenta ya jiyo mata maganar da takasa tantance sanadiyar rudewarta sai ganinta tayi a asibiti....!
WACE CE ITA..?? 38
Na Hauwa M. Jabo
Tana bude ido taga Su umma sun zagayeta Yar budurwar na zaune gefenta itada farahnax, sai nan ta tuna da abinda kunnuwanta suka jiyo mata, LAAA KINGA NA MANTA IFFO BANGAYA MIKIBA, KINA QAUYE AKA YIWA YAYA FARHAAN BAIKO DA SUHAILA..!!!! Hawaye ne suka wanke mata fuska shaaaaar, idan bata mantaba Wannan maganar itace qarshe maganar da taji sai yanxu da ta farka ta ganta a asibiti, ta motsa hannu taji yayi nauyi ta qurawa Suhaila ido mi yasa taji tana Sonta aranta?? Amma sai take ganin kamar ba sontane takeyiba tsanarta takeyi,?? Tanajin Suhaila har cikin ranta amma kuma tsanarta tayi yawa a zuciyanta. tana tsaka da tunani umma ta dafataa ta mata sannu, ta kalli umma tace hajiya miya faru?? Ya akayi mukazo asibiti?
Umma ta bata amsa da kin samu sauqi dai ko? suna haka sai ga nurse tazo ta dubata aka tabbatarda yanxu ba abinda yake damunta, illaa kawai ta rage tunani....
Ta tashi zaune anan farahnax ta bata labari muna tadi dake nake gaya miki an yiwa Yaya farhaan baiko da Suhaila sai kawai naga kin danne kai kina juyawa kika miqe tsaye sai kuma naga kin kika fadi sumammaiya, Suhaila ta katse wayar mukayo kanki muka kira umma taxo aka saka miki ruwa amma ko motsi daga qarshe sai Abba yace a kawoki asibiti, farahnax tace miyake damunki iffo?? Tunda kika dawo gida kika chanja ko su sukace miki ki riqa yi mana haka? Wallahi iffo banajin dadin ganin ki a haka, Dan zaman da mukayi na Saba da tsokanarki da labaranki Masu dadi, shiyasa ma na kawo Suhaila itama ki bata labarai sai Kuma haka ta faru, please ki saki jiki damu ke Yar uwarmuce kinji.!? Aranta tace da nasan abinda yake damuna Dana fada kodan samun natsuwar xuciyata..
Ta kallesu tayi murmushi ba komaifa, sai tayi shiru hawaye suka gangaromata,umma ta matso Ku bar min yarinta ta qarajin sauqi sannan Ku fara mata jarida. Dukansu suka saka dariya har iffaat din saida tadan murmusa.
Saida ta kwana daya da yini sannan aka sallamesu.
**
sun koma gida umma da farahnax suka sa iffaat gaba sai ta fadi abinda yake damunta. Amma ta murje ido tace bakomai koda yake ba komai din tunda ita kanta batasan abinda yake damunta ba, nifa tinda ta dawo Hutu banga dariyarta sau ukuba, umma tace nimadai banganiba umma ranar abbanku yace a kirata ta bashi labari amma tazo ba wani labari,
Iffaat!! Naam hajiya! Ki mana magana zama damune kike gajiya dashi ko kuma wani yake quntata miki ko kuma wani Abu yake faruwa a qauye??
Kawai sai ta fashe da kuka, kuka mai tsuma zuciya, ita kanta batasan sanadin kukanba, sukayita rarrashi har tayi shiru, ki fada mana minene idan mune mu gyara muryan ta a dishe tace wallahi Baku bane hajiya, nima wallahi bansan abinda yake damunaba haka kawai idan ina zaune sainaji raina ya baci ko kuma na riqajin inason wani Abu amma bansan ko miyeba qunci yamin yawa hajiya ta qara fashewa da wani kuka, sukayi chirko chirko, chan iffaat tace mamarta takeso .....
WACE CE ITA..?? 39
Na Hauwa M. Jabo
Umma ta nunfasa tace idan wannan ne damuwarki karki damu xamu nemo miki mamarki duk inda take, ta danyi shiru amma jifa jifa takan zubarda hawaye, bayan kwana biyu, muna zaune palo nidai kamar hoto ko nace gunki kawai cika wuri nakeyi. Suhaila ce ta shigo ina ganinta naji qirjina ya wani buga, da Leda a hannu, tana murmushi ta gaida umma tace nazo dubiyar mara lafiyane suka saka dariya ai ga tanan taji sauqi, ta zauna tamin ya jiki, na amsa mata inata kallonta har tadan tsargu, suhaila tace iffaat wallahi kinyi kama da qanwar babanmu sosai saidai tafiki haske amma hatta gashinki irin natane ke ko murmushinku iri daya tafiyarku ma iridayace ke hatta maganarku iri dayane ke komai naku iri daya, duk aka saka dariya har iffaat din ganin yanda Suhaila ta jajirce da bayani, sai kun sami lokaci kixo muje gidan mu ki ganta a gurinta nake zaune, iffat ta amsa da insha Allah....
*****
Iffaat dai bata gane karatu yanxu, gashi an mata nisa sosai abubuwan da bata yisuba a lesson take samu a namatasu, karatun ma haushi yake bata yanxu, zaman gidan ya gundureta, idan har aka zauna Idan ba hirar farhaan akeyiba bata taba samun sukuni a rayuwarta, wutar sonsa kullum Dada ruruwa take a zuciyarta amma har yanzu bata gane cewa she is fall in love ba...
Yar baqa qawarta tayi tambayarta har ta gaji sai tace ba komai, to batasan mi yake damunta ba bare ta fada,
Zaman birni ya gagare iffaat, kusan kullum saita xubar da hawaye wace irin rayuwace wannan?! ta matsa musu akan ita sai ta koma gurin iyayenta ta gaji da zama anan, aka buga sama da qasa amma taqi amincewa har suka gayawa abba,
Ranar yasa aka kirata ya tambayeta ko ana mata wani abinne tace ba abinda ake mata, iffaat bamu daukeki a matsayin Yar aikiba a matsayin Yar cikinmu muka daukeki wannan dalilin yasa har muka damuwa da damuwarki, muka sakaki makaranta Dan kema ki sami gata da yanci irin Wanda ko wacce yarinya take samu a gidan mahaifinta, iffaat kamar jiran abba take ta fara kuka kamar ranta zai fita, Abba nagode da dawainiyar da kukayi dani Allah ya saka da alkhairi, abba wallahi ni kaina bansan abinda yake damunaba rayuwata bata min dadi ba abinda yake burgeni a duniya komai haushi yake bani, banason naci gaba da wannan hali na damuwa kuma na sakaku akan shakkun kanku, wallahi kun min komai a rayuwa kuma na gode, wata qila Idan na koma qauyenmu tunda nasan yayyena suna zuwa nemana wataqil Idan nagan su in sami sassauci.
Amma Dan Allah Abba Ku mayar dani gida taci gaba da kukanta......
Tofa muje zuwa muji anya zata iya rayuwar qauye? Yama zaayi ta gane cewa soyayyah ce take damunta...??!
WACE CE ITA..?? 40
Na Hauwa M.Jabo
Abba Ku taimakamin ku mayar dani gidan mu, jikin kowa yayi sanyi yanda take kuka kamar ranta zai fita ta basu tausayi koni Jabo ta matuqar bani tausayi Dan saida nayimata qwalla, tabbas So balaeeee ne, yana zautar da mutum ya rasa mi yake masa dadi yama rasa gane kansa,! zaiyi loosing din control dinsa ne gaba daya, ko manya ya suke fafatawa da soyayya bare yarinya Yar shekara 15 irin iffaat da har Yanxu batada wani wayo bare har ta gane wane hali take ciki....
Abba yace To ki daina kuka iffaat zaakaiki gida dama Dan kada ya zama mune muke shiga haqqinki ba tare da mun saniba amma tunda kince bakomai kin zabi hakan shikenan, dukansu basu ji dadin tafiyar da iffaat zatayiba, amma ba yanda suka iya dole su saka mata ido, farahnax ma ta sameta a dakinta tana kwance bayan ta hada kayan ta, yanxu iffo tafiya zakiyi ki barmu?? Muka miki dan Allah da har bakya iya zama damu?? Ta kalleta tace sister wallahi ba haka bane bakumin komaiba, kawai rainane baya min dadi kuma bansan dalilin hakanba, kuyi haquri Dan Allah, anan dai sukayi hirar qarshe, koda iffo taqi sakin jikinta...
sun mata goma na arziki suka bata kudi masu yawa sannan akasa driver yakaita har qofar gidansu.
Shikenan iffaat ta baro gidansu farhaan.....
********
Iffaat a qauyen su,
Ashe yanzu balaen yake bata saniba, yanzu take qara shiga damuwa yanzu take gane cewa ganin iyayen farhaaan rahamane gareta, amma kuma still bata gano hakanba, ganin su da takeyi yana raqe mata qunci matuqa, ta sukukuce kamar ba itaba kai duk Wanda yaga iffaat sai yayi mamakinta bata magana, Yar gayu kam da take burin zama ta Riga ta zama, saidai so silent yanzu take yanxu. goggo har tana tsoro kardai ba abin kunya tayo aka korota birnin ba!!
*******
Watan iffat biyu a qauye ba walwala kullum fuskar nan a turnuqe kamar ta dijee dama dijee haka take ba sakin fuska su iffaat ne masu dariya, yanzu kam iffaat ta zama Yar baqin rai fiye da dijee..
Ranar iffaat ta tashi da ciwon cikinta har Yanxu goggo batasan ta fara period ba tasha magani ciwon ya fada mata tana zaune cikin runfar qofar dakinta da Dan tsinke a hannunta tana tsane a qasa taji sallama ta amsa batareda ta dago kaiba tsul goggo ta fito daki tana washe baki na dago kai na kalleshi, ke ihhatu bakiga yayanki yaxoba, koda na Dade ban ganshiba hakan bai hanani ganeshiba Yaya nane! Taje gunsa na fada jikinsa tna kuka shima dai yayi gwalla, suka zauna saman tabarma,
Yaya Ameen yake cewa goggo kinsan kuwa ba nan nakeda niyyar zuwa ba sai naga na biyo ta kusa danan nace bari na shigo qauyen namu in gaisheki, Ashe rabon naga Yar mamane kullum zancenki take mana, nayi murmushin jin dadi Dan uwa Rabin jiki ciwon cikinta tuni ya ware sai murna takeyi tana xubar da yan hawayen murna..
Nan take Ya kira Mama ya gayamata ai gani ya sameni yanxu mama murna kamar ta kasheta yau taji autanta munyi magana ta ita inatajin dadi,
Anan aka kitse akan gobe Yaya zaizo ya fafi dani daidai nan na Dan shirya, goggo ranta baisoba don iffaat ce rufin asirinta gata ba da bare jika.....
Available link for download