Saturday, January 28, 2017

WACE CE ITA 17 31

WACE CE ITA 17 31


 WACE CE ITA..??



WACE CE ITA..?? 17

Na Hauwa M.Jabo

Ya kalli ramcy kallon bangane mi kike nufiba, ya tambayeta WACE CE ITA?? Eh wace ce e ita.!! Wace ce ita kuwa bayan house girl dina, yayi guntun tsaki, ki kula kada ki tayar da ita bacci ba tada lfy, ya bata amsa ya fita abinshi, house girl ce hadda wani daukota,aranta tace yanda tasan farhaan da gyangyami ba yanda zaayi ya kula wannan qazamiyar yarinya, yarinyar da ko qirqar danki yanxu takeyinsa.
Ta gungura kekenta ta koma dakin farhan.

Farkawan iffaat keda wuya taganta a saman kujera itada tayi bacci a waje taja tsaki ko wane aljanine ya daukota ya kawota nan oho? taje lanbu abinta ta nemi abinda zai qosar da ita taci ta haye wata qatuwar  bishiyan mangoro mai sanyi bata dadeba ta fara gyangyadi da taga zata fado sai ta daura Dan kwalinta tayi yanda bazata fadoba.

Farhaan yayi baqo kuma  bayason yaga ramcy dan ba kowa yasa yana neman mataba, sai kawai ya janyoshi lanbu dama wasu takardune zasu cika tare, kusan awa uku sunanan suna aiki. bayan  sun qare suna tadi suna dariya, sai kawai sukaga abu kaman ruwa saman kan baqo amma ruwan yellow ne har dai ruwan suka jiqe takardun da suka cija gabaki daya, takardun da da suka sha wahala kamin su sami signed su chika, sun miqe lokaci daya suna kallon sama cike da mamaki da tsoro coz sun gane ba ruwa bane fitsarine hadda diminsa... farhaan ne ya hangota tana sharar barchi, wato fitsarin kwance takeyi, yaja tsaki kunya da takaici suka isheshi kawai yaja abokin sa zo muje ciki, abokin yace minene?? wallahi wani hatsabibin MONKEY muke dashi, shine ya mana fitsari Dan Allah kayi haquri muje ciki kayi wanka ka chanza kaya, sai kuma ya tuna ramcy tana ciki bayason ya gantane shi yasa yama kawoshi nan ga wannan sakaran abinda ta musu, yaqara jan wani tsaki, ya zaiyi dole tasa ya bude mai dayan sashen gidan yayi wanka yadauko mai kayan sa ya saka, abokinsa yanata dariya abin ya bashi dariya matuqa yace farhaan wannan  monkey da gani Dan iskane, farhaan ya murmusa ai hatsabibancinsa yafi wannan,  ta ciki na ciki bayan ya sallami baqo yazo lanbu yaci qaniyarta sai kawai yayi karo da ita gefen bishiya tana wasa da qasa, abinda ya gani ya bashi tsoro matuqa idonta sunyi suntum kamar jabo tayi kuka.!

Tana ganin sa ta kauda kai sai ya  yazo gurinta, ya tsuguna umma tana gaisheki tace kiyi haquri zaginda ake miki,kinji tace in baki waya kuyi magana, cox yasan duk abinda zaamata taji haushi baikai a zagi margayin babantaba, yayi ta mata surutuai ko motsi batayiba bare ta bashi amsa har ya gaji ya tafi.

Da yamma ta shiga gidan tasan farhaan bayanan sai ramcy zaune a Yar kekenta ta guragu tana cin Apple tana ganin iffaat tasha mur ta toshe hanci, iffaat saida taxo daidai ita ta wanketa da lafiyayyen mari, ta tureta saman kujera ta fadi, ta take qafar da aka daure ta murza sosai, koda batada nauyi saida ramcy ta saki wata qara Dan azabar da taji, ya kalleta irin kallon nan nata na wulaqanci, idan mijin naki ya dawo kice ya kasheni, ta koma lanbu abinta.

Farhaan ya dawo ya tararda ramcy a qasa tana kuka ya tambayeta tace ba komai gida kawai takeson ya maidata tana tsoron ta fada yaqara daku iffaat idan yafita ta kasheta haka ya maida ramcy gida....
   su iffaat sarkin gaba tun daga ranar bata qara yiwa farhan maganaba  ta daina aikin da takeyi, burinta kawai a maidata gida, amma ina ba hali,
Ranar tana zaune a sabon dakinta wato lambu cox yanxu kullum tana gun dare da rana ko tsoro bataji, dama tsoro bashida muhalli a zuciyar iffaat tana zaune ta hango wata qofa, koda taje ta daga an sa sakata an kulle ta bude sakatar tana budewa qofa ta wangale saiga ta taganta waje,....

WACE CE ITA..?? 18

Na Hauwa M. Jabo

Dama an hana mai gadi ya barta ta fita, itama an hanata zuwa gurinsa ba gunda take zuwa daga aiki sai aiki...
Sai yau cikin ikon Allah gata waje, Ta kalli gidan da tafito kallon sosai, gidane na gani na fada, kusan duk unguwar ba gidan dayakaishi tsari da girma, tayi yan kalle kallenta, ta samu  guri ta zauna anan taga yan mata nakai da komowa ko wacce kayan jikinta abin kallone fuska duk fenti ta kalli yanda suke tafiya kamar basason taqa qasa, aranta tace lallai birni birnine bata taba ganin yan birniba saiyau. Amma ita iya sanin ta karuwai ne basa yawo da gyale, amma taga wayannan manya dasu amma basa saka gyale kodai karuwanne?, haka dai aranta tayi ta saqe saqe har guraren yamma sannan ta koma cikin gida.!
Tana shiga taga farhaan da wata mata, aranta tace matansa uku kenan, lallai suna  qoqari, Bata  takansuba dama bayi tazo, wucesu tayi ta fita abin ta bawanda ta ko kalla balls gaisuwa, budurwar ta kalli farhaan waye wannan?? Yace watace,! to WACE CE ITA?? Mai aikice, amma batada ladabi shine kota gaida mutane, look hafsa! ba ruwanki da masu aikiin gidan mu please, ke kullum kikaxo sai kin kawo Qatar masu aiki haba, Bawai komai bane illah bayason rigimar iffaat yanxu sai ta zubar mai da mutunci,  ya qara da cewa kuma ma kurmace bata iya magana Dan ki fita hanyarta, tace Allah sarki,

Yaja budurwarsa ya wuce daki da ita, kwanan hafsa biyu a gidan. ranar iffat ta dawo daga kallon mutanen  unguwa da takeyi da yake tun lokacin ta daina mai magana tadaina yini gida hatta aikin ta dainayi, ta fado ba sallama,  sai hafsa ta kalleta a yamutse ke Dan kina kurma baki iya ishara da hannuba Ko uyayenki basu koya miki gaisuwa bane? Kai Allah wadaran halinki, ran iffaat ya baci amma guduwarta data korota tafi mata tsayawa masifa  Ta kalleta kawai ta mata tsaki ta wuce bayi abinta, Dan abinda takeji ya matseta!! ta qare ta fito tana waqarta ta badi ba rai soyayyah jigon rayuwa.......,

 nan ma hafsa ta qara magana, wallahi sai na sa farhaan ya koreki duk masu aikin gidannan suna gaisheni amma bandake Mara kunya kawai, waike kurmako?? da ganin idonki nasan ba kurma kikeba iskancini kawai kurmace ke waqa .dama farhaaan duk masu aikin da yake mafi yawa yan matanshi suke sa yana korarsu, wasu kuma baqin halinsu kesa ya koresu, iffaat har zata tankata nan ma sai ta mata kallon banxa tayi tsaki ta wuce abinta. hafsa kamar an tsikareta dama idan kayi masifa akayi banza dakai yafi haushi, ta janyo iffaat ta wanketa da mari....

WACE CE ITA..?? 19

Na Hauwa M. Jabo

Habawa!! iffaat bata dubu girmar matarba Dan kobata kaiba zata kai 25yrs ita kuwa yanxu take Shiga14, itama ta wanketa da wawan mari daidai shigowar farhaan, kee iffaat lafiyanki? hafsa ta riqe kumatu tana mamaki, yau yar aiki take dukanta, tasan tafi qarfinta Dan ubanta mashhurin mai kudine itama kawai tanason farhaan ne take biyoshi har gida amma tafi qarfinsa, yana zuwa daidai ita hasale a ya wanketa da mari biyu  masu kyau saida ta fadi, ya nunata da yatsa, ina Dada jaddadamiki ke ba kowa bace illa mai aikina kuma bazan maidaki gidankuba anan zaki ci gaba da zama,  kinamin bauta, idan kikayi ba daidaiba am always ready na babbalaki,dama sabida umma nake raga miki so naga ba amfanin haka, qara in nuna miki ni waye, stupid girl kawai ya, rungume hafsa yana bata haquri, hafsa ranta yayi fari Sol Dan yayi hukuncin da ya mata dadi, ta kuwa narke a jikinsa farhaan mai farin jinin yan mata.

Ta miqe tsaye taja ta toge ta rasa abinda zatayi ta rage haushi kuma ta bashi haushi ya sallameta amma ina kwakwalwanta baya aiki ko kadan hasalima tausayinsa takeji,

***

Tafita daga gidan taje waje kallon yan mata, wata yarinya da take yawan gani tana wucewa yarinyar ta shiga ranta har takeji ina mazata yi qawance da ita, wata zuciyar tace a haka zatayi qawance dake kina duqun duqun, ta kalli jikinta ta tuna tafi wata daya a gidannan amma duka wankanta uku, kamar yan makarantar su jabo basa wanka daga frdy sai frdy..

Ta kalli kanta aranta ta fara imagine irin gasunan tare da yarinyar suna driving a mota Habawa ta gyalgyale da dariya hadda buga qafa a qasa, har ta manta da an mammareta ita kadai kamar zararriya, lallai idan har tayi qawance da yarinyar chan Yar baqa ta qare qawance a duniya, tana nan zaune taji kamar maganar farhaan saida hanjin cikinta suka juya dan kuwa shine, lallai kamin ta ruga ta shiga gida zai iya hangota, kamar monkey dinda ya kirata haka ta Dane bishiyar da take zaune gurinta farhaan yazo daidai bishiyar ya zatsa yana danna waya.....

WACE CE ITA..?? 20

Na Hauwa M. Jabo

Yaci gaba da wayansa saida ya qare kamar zai daga kai ya ganta amma hankalinsa na gun budurwar da yake tsarawa a waya, bata gane mi yake cewaba Dan da English yake magana, ya wuce kamar da second 30 ta sauko ta shiga gidan da sauri ta kulle qofar lanbu taje gurin zamanta tana addua da Allah yasa bai gantaba, idan ya ganta tunda yace bazai maidata gidaba ya zatayi, zai kulle qofarne ya hanata fita ko ina gashi tanason tayi qawance da yar baqar yarinyar da take gani tana wucewa. 

Tana nan zaune Tana Zane a qasa ya kwala mata kira taje ta turbude fuska, yace taje hafsa na kiranta, batamai musuba ta wuce shima yayi mamaki sosai yanda ya wasketa da mari batace komaiba, aransa yace kodai ya fara nasarar natsar da itane, hafsa a Palo zaune, wai ta dan qasa mata qafafuwanta da ruwan xafi, ( inaga ta kusa fara period ne coz yan chinar skull dinmu haka sukeyi kuma zakiga sun Dan sami sauqin ciwon cikin) na watsa mata harara, banganeba, tamin bayani shiko gogan yana tsaye ya rungume hannuwansa, nikaina jabo nayi mamakin iffaat data amince da aikin, ta zauna ta riqa juya ruwan turinisu suna dukan qasar qafar hafsa har suka huce ta zubar ta dauko wasu ta mata daqowar da hafsa zataye ta hanbare iffaat ta fadi xaune ruwan suka zube a jikinta duk ta jiqe amma ruwan ba wani zafi sosai, farhaan ya kallesu baice musu komai ba, yaci gaba da kallon ball dinsa, karo na uku ta dauko ruwan zafin da gangan  iffaat ta juye matasu a qafafu, hafsa ta tsallara ihu, iffaat ta miqe tsaye da qarfi tayi gefe farhaan yazo da sauri yana duba qafar ba abinda tayi a Zahiri amma tana zugi daga ciki iffaat tayi tsaye tana jiran hukuncin da farhaan zai yanke mata da sauri  ya kira Dr. hafsa sai aikin kukatakeyi, yana rungume da ita tanata ihun, yace iffaahh. Ta watsomai idonta da gani tadan tsorata ya akayi haka?? Ta fuske kamar da gaske, naje zan juye ruwan sai kawai tasa qafa zata shureni saita shure ruwan suka juye mata a qafa, harga Allah ya yarda cox yaga yanda ta shureta karo na farko, ya jinjina kai, duk da baiji dadiba amma yasan iffaat batada laifi,......

Dr yazo ya dubata ya bata
magunguna, tace zata koma gida kada yar aikinsa ta kasheta, baiji dadiba cox duk cikin yan matanshi hafsace kawai take iya jure jarabarshi, cox ita sonshi takeyi so duk wahalan da zai bata tana jurewa sauran kuma, kudi kawai sukeso,
Yakaita gida, ya dawo bai kula iffaat ba ya wuce dakinsa sai yanxu ya kula dakin yayi kacha kacha ya kwala mata kira, ke zaman me kike a gidannan?? Kalli dakina kalli toilet dina! Miye amfanin kine??

WACE CE ITA..?? 21

Na Hauwa M. Jabo

Dole kiyi aikinda aka kawoki kiyi idan har kinason amaidaki gida, so zabi ya rage naki, ko kiyi aiki a maidaki gida ko kuma kiyi ta zama anan har qarshen rayuwarki.  taga gara tayi aikin ya maidata gida.

***********************

Yau watan iffaat biyar a gidansu farhaan inda sabo yaci ace ya saba da halinta ya kawo budurensa daidai har 8 suna chin uban juna Ita dasu, kuma ko wacce sai tayi nasarar daukar fansar abinda suka mata ta hanya kala kala, kuma farhaaah Sam baya ganewa, ita
Har yau ta kasa gane cewa ba matansa bane matan banxa ne da taga sunfi hudu sai kawai aranta tace auri saki yakeyi, irin na wani alhajin qauyensu da akace auri saki yakeyi, kullum sukaje Gidansa kallon TV sai suga sabuwar mata a gidan akace auri saki yakeyi, anan ta gane halinsu daya da farhaan...

*********

Yau dai iffaat an tashi ba lafiya zazzabi yake damunta da wani gwauron ciwon ciki, har bacci ya dauketa tsakar bacci ciwon ya tayar da ita taji danshi danshi a qasanta dubanwa da zatayi sai taga jini Habawa ta fashe da kuka koda ta tashi ya mata kache kace a jiki Ashe ya Dade da zuwa bata kulaba, tayi Saa farhaan yana palo yana kallon ball ta fito a hargitse tana kuka, ta nuna mai jininta fa na xuba, ya kalleta habo kikeyi?  aah ta  gun fitsarinane, kunya ta kamashi, shi wace irin yarinyace umma ta sashi dole zama da ita wai mai aiki gashi ta zame mai jaraba, yayi tsaki yana kall ball dinsa zaa katseshi, to kije daki zan siyo miki magani yanzu, yama Dr waya akawo mai pad da maganin ciwon cikin na mata bada jimawa ba Dr ya kawo mai, ya kirata amma ba amsa ya gaji yayi banxa da ita, sai da ya qare kallon ball dinsa ya miqe tsaye sai maganin ya fadi sannan ya tuna da wata iffaat ba lafiya yaje dakinta da yake yana mura baiji qarnin da dakin yakeyiba, koda yajee ya ganta ta dunqule a qasa sai juyi takeyi, duk jikinta ya baci, ya rasa yanda zaiyi idan ya dauketa zata bata mai jiki ya waya da  Dr waya shiru  bai daukaba, ya tsaya gabanta ganin numfashinta na hawa da sauka kamar zata mutu yaji tsoron tamutu a gida da zamo mai aiki, yaqara yima Dr. dinsu waya yace mai normal ne na farkone ya bata maganin da ya kawo zata warke kada ya  damu, ya dagata  chak ya yakaita bayinsa ya wanke mata jiki ya rasa yanda zai chire mata tufafi tunda duk sun jiqe yaje dakinta ba kayan da zai saka mata duk saman gadonta suke kuma duk ta batasu da jini, yaje dakin farahnax qanwarshi ya memo wata jallabiya baqa yazo ya rufe idonsa Dan kada ya ganta ya chanxa mata kayan jikinta ya....

WACE CE ITA..?? 22

Na Hauwa M. Jabo

Ya bata magani dagyar tasha ta amaryar ya qara bata wani, yace ta daure ta saka wannan abin pad tace bata iyaba, ya kalli bayan ledar yaga yanda ake sakawa ya hada mata ya bata ta saka,  pant ma a kayan farahnax ya daukoshi, yace ta kwanta dakinsa dakinta ya harqitse tunda batada lafiya, tanashan magani tuni tayi bacci,
Bata farkaba sai bayan laasar tafito Palo tana dingishi zata tafi dakinsa ya kirata zonan, ya jikin ta amsa a kasalance, naji sauqi da gani hajiya iffaat anji jiki Dan har idonta sun fada, tayi wani iri da ita, ya kir Dr. ya miqa mata waya Dr ya mata bayanin yanda xatayi komai kuma kada ta damu duk mace mai lafiya tana wannan abin sabida haka ta godewa Allah

 ya fada mata zata iyayin kwana bakwai tana xubarwa, likita jinina bazai qareba?? No wannan ba jini bane ciwone yake fita idan bai fitaba idan kinyi Aure  bazaki haihuba ko bakyason haihuwa??  inaso mana, him wayaga iffaat da ciki,  yadai mata bayanin komai sukayi sallama, ta bashi wayarsa, ta wuce daki koda taje duk an tattara kayanta gabi daya da zanin gado duk babu, an saka wani, sai yanzu ta tuna yanda tayi kacha kacha da ko ina...

Iffaat saida tayi kwana biyar sannan ta kammala, farhaan ne yasa aka kai mata kayanta wanki.
Wannan ciwon shine mafarin fara shirin iffaat da farhaaah..

Tunda ta fara ciwo sai yau ta fita waje kamar yanda ta saba, tana zaune sai ga black girl dinnan ta wuce qamshinta ya doki hanchinta aranta tace anyi yar gayu anan gurin, ta qare kalle kallenta ta shiga cikin gida bayan ta koma gida tana dakinta zaune tunaninta daya ya zata zama yar gayu irin na yar baqar yarinyar nan, taje bayi ta kalli madubi, sosai ta bude haqoranta taga yanda sukayi laka laka a qasa ga wata tsatsa da sukayi tofa bata wankewa fiye da haka ma sai tayi, batasan yanda zatayi dasuba suyi haske irin na tsohuwar matar farhaan ramcyba, cox ramcy akwai wushirya kuma da  fararen haqora Tass dasu, tayi tsaki ta qara gaba...

Ranar ta fito Palo, karo na farko da ta taba tsayawa kallon TV tunda tazo gidan nan sabida farhaan kullum ball yake kallo itako batason ball a rayuwarta, tafison indiya an qare ball ne Anje talla sai kawai ga tallar signal, mouth Clean ne mai kyau, taga yanda ake wanke baki sai ta tuna ta tabaa ganin farhaan yana wankewa har ta tsaya kallonsa, taje bayin dakin ta nemi mouth clean din koda ta duba sai taga exactly irin Wanda aka nuna a TV ne, tayi murmushi Ashe haqoranta zasuyi fari irin na matar Tv ta Dan barashi a brush tana wankewa yana jini duk da ya mata xafi ta daure cox tanason ta zama yar gayu irin na yar baqa sunanda  ta sanyawa yarinyar kenan, iffaat dai haka tajuri yi brush kullum ko nace duk lokacin da abin ya motsa sai tayi cox.......

WACE CE ITA..?? 23

Na Hauwa M. Jabo

Cox a rana sai tayi brush Sau biyar baayi kwana sati day ba  suka fara cire wannan lakar, kuma tsatsar ta fara bacewa,
Ranar tana zaune tana charafke sai ga farhaan, dama bata gaidashi idan yazo ya zauna yace yau kuma TV ake kallo da  charafke,  ta juyo ta kalleshi tayi dariya, tace eh so nake in zama yar gayu irin na matan Tv ya kalleta sosai sai yau ya kula tana da wushirya,idan ba idonsa suke masa gixo ba yaga haqoranta sun cire wannan laka lakar na da,.

Yace gashi kuwa su Umma zasu dawo anan zasuyi azumi, Dan murna batasan lokacinda ta tashi tsayeba Ashe nayi kusa tafiya gida,? Naga su dije da rukayya da goggo, tanata dariya, lallai gaskiya ya hango, haqoranta sunyi haske, kinga idan kin tafi kin huta dani ko, ta kyalktale da dariya saida kumatunta ya lotsa, ai zama da mugu irinka sai An shirya kamaci arzikin ina tausayinka, shi yasa duk matanka suke guduwa duk matar daka aura sai ta gudu, kalli fa cikin wata biyar saida kayi Aure 8 lallai yarinyar nan batada wayo,! ita ta dauka duk matanane kena, hahaha nine mugu iffaat??  babba ma kuwa. Ta fada ba tareda shakkar komaiba bakya kunyar fadamin haka a gabana? lallai kin girma, ta kalleshi ta tabe baki, ai gaskiya na fada, nima yanzu zan shirya suna dawowa sai in tafi gidako?  Taci gaba to yanxu kai zaka mini dunkin sallah ko hajiya??

Yagyara zama ni xan miki ai ni kike yiwa aiki ko? Eh Kaine maigiana, ta juyo tana fuskantarshi kasan wani abu,?? Saikin fada, naga aminar baba sule idan ta dawo aikibirnib sai ta dawo da kayan gayu, tufafi sabbi qanzon shinkafa sabulai, abubuwa dai da yawa na birni, ni ina zan samu?? yayi murmushi dama tanada surutu haka? Yace kema da kina min aiki da kyau da duk zan siya miki abubuwan da kika lissafa hadda qari ma zan miki, amma ke bayan tsiwa da rashin kunya da zubar min da mutunci  ba abinda kika iya LA ilaha illallahu, yanzu duk aikinda na maka haka zakace? kallifa baka taba dukana na ramaba, au da ramawa kikeyi? Taaaab wallahi a qauyen mu komi girman qato idan ya dakemu sai mun rama, kai hadda shugaban yan sandan garinmu ya dakemu mukaje gidan sa da dare muka fasa mai mota, ya fito da I do da gaske kikeye??
Ta  qara gyalgyalewa da dariya sai tamai kyau, wallahi da gaske nakeyi, kicemi ke yar taaddace...!

WACE CE ITA..?? 24

Na Hauwa M. Jabo

Nan ma dariya tayi ai baka sannibane, ta fara bashi labarin taaddancin da takeyi a qauye, ya jinjina mata sosai kuma ta balaen burgeshi Dan yanason yaga mace mai kamar maza, anan ya gane duk abinda yan matansa suke fada akanta gaskiya ne,

Abinda yaxo mishi gona hafsa da tayi da ruwan zafi yace Kena da gangan kika xubawa hafsa ruwan zafi? Ta kalleshi ta kanne mai ido ai muguwace, kuma ita tafara xubamin ruwan kana kallo bakace  komaiba, sannan akanta kamin mari biyu ita ma tamin daya shiyasa duk cikin matanka nafi tsanarta, kuma da gangan na zuba mata ruwan,? Ke  yanxu data qonefa?? Aaaaaaaa miya dameni badai na rama ba!! Ya kalleta da kyau yarinyace sosai kuma lallai batada wayo ko kadan ga shegen surutu...

To yanxu dai ki riqa aiki da kyau zan siya miki duk abinda kikace waccan qawar taki tana tafiya dashi qauye idan zaki tafi gida, yatashi ya wuce dakinsa, yabarta tanata zuba, aranshi yace lallai da yana kula yarinyar nan da ta debe mishi kewar qanwarshi farahnax Dan ya kula akwaita da shegen surutu ga saurin sabo saidai sabon baya hana tama mutum rashin kirki Dan yaji yanda take danbe da qawarta dijeee !!!

Kamar kullum bayan fitar farhaan taje S pool tayi wanka da yake shi yake debe mata kewar kogin garinsu, tayi wanka abinta ta qare tabi ta lanbu taci abinda xataci ta fita doguwar rigar da farhaan ya bata  lokacinda batada lafiya ta saka sai ta mata kyau sosai, tana zaune tana wasa da qasa sai ga yar baqarta tazo tayi kwalliya baqinta sai kyalli yake tayi kyau tsab tsab da ita da takalminta masu tsokane duniya, ba abinda yake burgeta irin yanda take wani Dan tuntu saman kanta ( acucu maza take nufi) yana burgeta matuqa amma batasan yanda zatayishiba ta qare zamanta, ta koma gida da tunanin yanda zatayi wannan abin na saman kan yar baqarta, tayi tunanin Idan ma gashintane zaiyi irin na Yar baqa, tinda gashinta yanada tsawo sosai tunda tazo gidan da kitso bata tsefeshiba.

WACE CE ITA..?? 25

Na Hauwa M. Jabo

Tashiga dakinta ta zauna ta tsefe amma saida tayi kuka dan zafi kuma gashi ba kibiya duk ya harhade ko gida  kullum sai tayi kuka idan ana mata tsifa, yauma saida tayi taje ta wanke da man da taga anyi hoton qashi jiki haka datti ta riqa zuba kamar an kwaba qasa, haka tayi ta xubarda daddi har yayi fess dashi kamar bana iffaat ba, matsalar daya ba tada mataji kuma ba tasan yanda zatayi irin na yar baqaba, sai ta fito Palo  tana goge gashin farhaan ya kalli gashinta aransa dama tanada gashi haka, ya zauna yace dama kinada gashi shine baki kyarawa, tace wallahi parhuun zafi yake min.! Ya kalleta tanata kiciniya da gashi yace ya sunana? Tace Parhuun mana haka naji kowa yana fada, ya kwashe da dariya saida yayi kwalla wai PURHUUN yarinya katki bata min suna sai nanatawa yake PURHUUN lallai wato kusan shima bata iyaba gaskiya anyi baqauya anan yace to ba haka bane farhaan ne, ta dago kai tace Parhan, yace aah farhaan, parha, ke kalli bakina, kice far, tace, par, kalli ki  haqoranki akan lebenki zaki Dora sai kice far, takuwa yi tace far yayi dariya yauwa kinyi daidai, sunana  farhaan,ta fada daidai tace Dan gayu ko sunan ka sai ka koyamin. Ta bashi dariya wai Dan  gayu, so funny, tace to yanxu gayamin yanda ake wannan abin a saman kai yayi sama sosai, yace ni ban iyabafa banmasan mi kike nufina, LA ilaha illallahu, ta to saki gashin ta toshe baki babba na qarya, wallahi ko wasu a matanka kamin ka sakesu nagansu dashi kace baka sanshiba, yayi dariya lallai yarinyar nan case ce, ni nake qarya?? Waima waya gaya miki matanane?? Ta zunburo ta kama gashinta ita burinta a mata irin na yar baqa ta hanya,tace to miye naka? Abokainane ko ban fada miki inada abokai mataba, ta saki gashin kanta ta qara rufe baki da hannu, shine kake tabasu? Hmmm!! Ta tabe baki Mudai garinmu duk namiji mai taba mata Dan iskane, ko wasa bamayi da maza duk iskancine garinmu, kaga da garinmu kake da nace maka Dan iska, keeeee, nine dan iska,?? ta zaro ido ai ban fadaba.  nace da garin mu kake.. aranshi yace ko inane wannan iskancine, yace to a birni wayewace ba iskancineba, ya fuske ya miqe  zai fita, baka gayamin yanda akeyiba, sai na dawo zan gaya miki...

A hanyarshi ta dawowa yayi karo da wata tayi acucu maza sai ya tuna da alqawarin da yayi,ya siyo mata ribbon  manya da mataji da man kai ya kawo mata.. 

Tanatajin dadi zata yi irin na Yar baqa, baanan kizo ke saqarba bata iya sakawaba ta kuwa fara hadashi da Allah, ya koya mata shi ba iyawa yayiba, yana mamakin yanda take mai kamar wani saarta yanaga ta mance WACE CE ITA.!! Yayi tsaki ke kada ki dameni kinji, na siyo miki kuma ni zan saka miki?  duk ma yan matanshi basuda gashi irin nata duk qarine sukeyi, ya zauna yaci gaba da kallon ball dinsa, dama iffaat akwai naci akan abinda takeso. tazo tana hadashi da Allah tana mai shagwaba abin ya burgeshi.. 

Yayi tsaki aranshi yace yarinyar ta fara rainani, ta kuwa miqamai gashi ta zauna ya rasa yanda zaiyi to ki taje mana ta fara tajewa tana gwalla Dan duk ya sarqe tanayi  yana shafa mata mai har ya taju yayi kyau gashin yana gyalli abinka da gashin fulwni sai Wanda ya gani,ya karbi gashin ya kasa tattarshi yace ta tattara da kanta ya nuna mata yanda zatayi ta tattara, to aike basai kin saka irin nasuba tunda gashinki yana da tsayi sosai, Allah ko?  eh mana,  haka ya taimaka mata tayi parking dinsa kuma yayi irin yanda take so, yanxu kasan mi nakeso? Yace Aah, akwai wasu kaya da ake sakawa sai ayi wannan abin sai ayi kyau a zama yan gayu  idan xantafi gida zaka siyomin?  nama taba ganin abokiyarka da irin su!  Ke ni ban ganesuba, kuma ki sani duk suna cikin kayan sallanki, eh na yaddda ta amsa tana zagwadii....

WACE CE ITA..?? 26

Na Hauwa M.Jabo

Bayan ya dawo, ita duk wautarta yau zai siyo mata kayan taga wayam hannunsa ba komai, laaa farhaaah  Yaushe zaka siyomin kayan gayuna?  irin na abokanka,? Ya harereta bakida kunyako kina kiran sunana. Ko bangirmekiba. yi haquri  Mixance makato?  ta fada irin ta matsu dinnan taji zancen kayan gayu, look ki bari zan siyo miki kawai kamin ki tafi gida, yayi niyar yaje da ita a aunata gun mai dinki amma ina yana tsoron ta kwafsa mai wannan hargitsatsaiyar wataqilama taje ta nemo magana, to kawai tace mai amma ranta baiyi dadiba ta wuce daki ta zauna, ta fara tunaninta na zama gayu irin na Yar baqa iffaat yanxu batada buri irin taga ta zama Yar gayu, Niko inason ganin iffaat da gayu, aranta tace gayufa dole saida wanka, taaaab yanxu kullum sai tayi wanka kenan.??  idan ba wanka ba gayu, ta tashi ranar farko data ji tayi wanka Dan raayin kanta, 

ta fada wanka tayi wanka da ruwan zafi ta wanke dattin wafafuwanta sabida bata yawo da takalmi ko lanmu haka take tafiya ba takalmi tana wankewa ta tuna da qafafun hafsa lokacinda tasata gashi, sumul  sumul qafar yan gayu ba kaushi, ta wanke iya yanda zata iya, ta fito ta saka yan tsumma karonta.. Tayi bacci anan tayi mafarkin ta zama Yar gayu, tayi qawance da Yar baqarta, ta farka ta fito Palo cin abinci bata dadeba sai gashi ya kawo mata kaya English Wear ne, ya nuna mata wayannan kayan kike nufi?? Sauran nakai dinki duk na sallah ne amma, Ta kallesu a tsorace ita a qauyensu idan mace ta saka wando zaace mata yar iskane so bazata sakaba, data fada mai yayi dariya sosai wato qauye balaee ne, qauyanci masifa, yace ki riqa saka wannan a gida idan zaki fita saiki saka wayanda bana yan  iskaba. OK bari in saka ka gani, anan yaga zata cire kayan jikinta  no ki shiga daga ciki mana, ta kwashi kayan ta shiga daki da gudu ta saka wandon yafito da ita ainihin ita sai Wanda ya gani mazaunan suka fito hips din ma ya fito, da yake dukiyar fulanin yanxu take fitowa yayi dan tudu kadan sai head dinsa ake gani ya fito saman rigar,  ta fito da gudu tana dariya na fara xama yar gayuko? farhaaah ya kalleta tashin hankali, 

Ashe babyn nan ta hadu a ransa ya fada, dukda cewa ba daidai ta saka kayan ba amma sun mata kyau, kalli nayi kyau, sosai kin ganki kuwa, tace kamar ba yar aikiba ko, yace sosai kuwa, tana ta dariya ta janyo gashinta da yake ta cire riboon garin saka tufafi wai dole sai yayi mata yanda akeyi dinnan, no ki bari in miki hoton tarihi kuma na turawa umma taga yarinyarta ta fara zama gayu, nan ya sa tayi wannan tayi wannan idan tayi wani style sai yakai zauna Dan dariya, qarshe yace to tazo ya dauketa ita dashi ba tare da damuwaba ta kwanta a qirjinsa ya daukesu photo tana dariya duka dimple dinta sun lotsa gwanin ban shawa,  kawai daga kan da zasuyi sukaga hafsa kamar daga sama, ta kalli kayan jikin iffaat ta watsa mata harara, ta riqe kunkumi wai farhan na tambayeka waye wannan yarinyar??  kawai fada min gaskiya, ya kalleta kallon bangane mi kike nufiba, sau nawa ina fata miki WACE CE ITA! Amma kina min magana wai iri, hafsa ranta ya gama baci  iffaat kuwa dama batayi ta kantaba, murnar kayanta takeyi batama gane hafsarba yana juyowa tace Yaya farhaaah yaushe zaka kawo min kayan sallah? Ya kalleta ita ba abinda ya dameta sai su umma sun dawo,

Kamin ya juyo hafsa ta fita Yabi bayan  hafsa, itakam ta dauki kayanta ta je dakinta,
Kamin ta tada mota yasha gabanta yace mai gadi ya kulle gate, hafsa kuwa anriga anyi fushi, ya bude motar ya janyota jikinsa, ya rungumeta yana shafata a hankali, miye na fushi, hafsa??
Ni kawai ka fada min WACE CE ITA please!!

WACE CE ITA..?? 27

Na Hauwa M. Jabo

Wallahi na gaya miki WACE CE ITA, ba kowa bace illa house girl dina, house girl take saka English Wear?? house girl kake rungumewa kana photo da ita?? Haba farhaaah kada ka mayar dani qaramar yarinya mana! no hafsa wallahi ba haka bane kin gane yarinyar batada wayo ko kadan kuma zata tafi gauyensune da umma ta dawo shine na siyo mata tufafi,  kuma wallahi kinji na rantse umma tace in siya mata duk abinda take so, tunda ta kusa tafiya, kiyi haquri wallahi ba komai tsakanina da ita, mi zanyi da mai aikina, haba aiba class dina bane, yarinyace fa qarama ya kanne mata ido, ai dama ka gware a sweet mouth, yayi kissing din gefen fuskarta, muje daga ciki tana jikinsa har suka shigo, dakinsa suka wuce nan dai yachi gaba da rarrashi har mai afkuwa ta afku, nidai jabo idan zasuyi labewa nake sai sun kammala inshigo ciki, Allah ya shirya mana zuria kwanan hafsa biyu a gidan amma farhaan bai bari sun hadu da iffaat ba Dan a labarin data bashi ya gane ba qaramar yar taadda bace kuma bata mantuwa bare yafiya, daukar fansa gunta wajibine..

**********

Ayau ne su umma zasu dawo farhaaah Dan dole  ya karbo mata tufafin da ya dinka mata atamfa biyu les uku, yace ta saka idan su umma sunzo ya bata turaruka da s

Available link for download